Turkish
   Persian
   Arabic
   English
   French
   Dutch
   Russian
   Bengali
   Hausa
   Urdu
   Tajik
   Malay
   Indonesian
   Spanish

 

Sakon hajjin bana na maigirma Ayatullahi  sayyid Ali khamna,i, shugaban juyin musulunci na jamhuriyar musulunci ta Iran

 

   2006

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai

 

Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Muhammad (S.A.W.A) da iyalansa tsarkaka. Da sahabbansa masu gaskiya.

 

Aikin hajji kamar kowace shekare  wanda ya cike da tarbiyyar ruhi ya sake zagayowa wanda yake wata babbar damace ga duniyar musulunci. Duk da cewa zukata daga sassa daban-danban suna cike da shaukin zuwa wannan wuri mai alfarma, amma  "yan kadan ne kawai suka samu  dacewa da zuwa wannan wuri mai tsarki, sannan wannan yana daga cikin abin da ya kara wa wannan idanuwa mai bubbuga albarka ta har abada.

 

  Haduwar 'yan uwa musulmi daga ko'ina daga sassan duniya acikin dakin masoyi, ta bangare guda wannan yana kara fuskantar da al'umma zuwa ga mahalicci, ta bangare guda kuwa  yana hada masoyan da suka nisanci junansu, saboda haka wannan yana samar da nishadi na musamman tsakanin al'ummar musulmi.

  Tsarkaka daga daudar zunubbai baki daya acikin dukkan ayyuka a   kowane wuri, saduwa da ubangiji, duk da yake acikin 'yawanuka takaitattu, amma babban guzuri ne ga dan Adam. Sakamkon ladubba da dukkan abinda ayyukan hajji suka kunsa duk don mutum ya samu wannan ganawa da ubangijinsa ne wadda sakamakon haka zai dandana wani zaki na musamman, sakamakon haduwarsa da ubangiji.

    Ta bangaren siyasa kuwa, abu na farko da aikin hajji yake nunawa shi ne hadin kai tsakanin al'ummar musulmi. Nisantar al'ummar musulmi tsakanin juna shi ne yake janyo makiya su sanya ransu wajen cin nasara akansu, sannan wanna ne yake taimakawa wajen kyankyasshe kwan sabani a tsakanin al'ummar muslmi.

  Al'ummar muslmi ta ginu ne daga mutane daga kabiloli da harsuna daban-daban, sanann daga mazhabobi mabambanta. Wannan bambance-bance wanda ya samu ta hanyar bambancin wurin zama ta yadda ya kasance acikin wani yanki na musamman a bayan kasa. Wannan zai iya zama wani abu ne  wanda zai karfafa wannan al'umma ta wata fuska. Sannan kayan tarihin da suka yi tarayya a tsakaninsu zai taimaka wajen hada junasu, sannan su yi amfani da baiwar da suke da ita a matsayisu na 'yan Adam wajen tabbatar da gurinsu.

  Yan mulkin mallaka tun farko sun kula da haka shi ya sanya suka yi gaggawa wajen raba kan al'ummar musulmi.

  Shugabanni masu mulkin mallaka sun riga sun sani cewa, idan duniyar muslmi ta kafu, to babu shakka mulkin mallakar da suke yi ta hanyar tattalin arziki da siya zai kawo karshe. Saboda haka ne ta kowace hanya suke kokarin suga sun kawo sabani acikin  al'ummar muslmi, a karkashin wannnan lemar ne suka yi amfani da jahilcin mafi yawan al'ummar musulmi da shugabanni masu ko in-kula na siyasa da al'adu, ta yadda suka samu damar mallakar kasashen musulmi ta hanyar siyasa da al'adu.

  Dankwafar da kungiyoyi masu neman 'yanci a tsawon karnin daya gabata a kasashen musulmi, sannan da gaggauta mallakar kasashen musulmi ta hanyar masu mulkin mallaka, da samar da, ko karfafa hukumomin kama karya na kasashen musulmi, da wawashe dukiyoyin wadannan kasashe, da kawar da al'ummar wadannnan kasashe, da dankwafar da kasashen musulmi ta yadda kada su cigaba ta fuskantar fasaha da kere-kere, wannan kuwa duk karkashin inwar raba kan al'ummar muslmi ta yadda har yakan kai ga yakar juna.

  Amma bayan farkawar musulmi  wanda ya kai kololuwarsa sakamakon samar da jamhuriyar musulunci ta Iran, wannan ya sanya masu mulkin mallaka suka hadu da babbar barazana. Da kuma gazawar tunanin siyasa na kasashen yammacin duniya, sannan da gazawar akidun kasashen yamma wadannan da suke ganin ta wannan hanyar ne kawai al'umma zata iya cin nasara. Farkawar musulunci ta samu kafuwa acikin zukatan al'ummar musulmi, sannan da gazawar masu mulkin mallaka wadda ta faru a wurare masu yawa wajen gamawa da wannan halitta da take cikin zukatan al'ummar musulmi ta son musulunci, wannan ya rayar da zukatan al'ummar musulmi.

  Idan aka kalli Palasdin a yau wanda gwamnati wadda ta tsayu akan kwaton yancin Palasdin, idan muka kwatanta da rishin galihu da halin kaka na ka yi da alu'ummar palasdin suka kasance aciki, sannan idan aka kalli Lebanon inda musulmi suka bayar da rayuwar ta yadda suka fuskanci kasar Isra'il wadda ta mallaki manmanyan makamai tare da taimakon Kasar Amurka da kasashen Turai, suka iya karya wannan kasa tare taimakon Allah, idan aka kwatanta Lebanon a lokacin da Isra'il duk lokacin da suke so ba tare da wata wata ba, zasu iya yin duk abin da sukeso.

   Idan muka kalli Irak wadda mutanenta masu kishi suka buwayi Amurka, sojoji da 'yan siyasar Amurkja wadan da suke hura hanci akan mallaka kasar Irak, a yau suna cike da fuskantar matsaloli daban-daban da suka shafi soja da tattalin arziki,  idan kwatanta wannan Irak da Irak a lokacin Azzalumin shugabanta  wanda ya kasance yana shan jinin bayin Allah.

  Idan muka kalli Afganistan wadda dukkan alkawullan Amurka da kasashen Turai suka kasance karya da yaudara, sannan suka kai hari tare da sojojin kawance wanda yana da wahala a sami kamarsa a tarihin kasashen yamma, bayan ruguza kasar Afganistan da haifar da talauci ta kissan al'umma a wannan kasa, da karfafa kungiyoyin boye masu samar da muyagun abubuwan sanya maye, babu wani alheri data samar wa wannan kasa ta Afganistan.

  Daga karshe tare da la'akari da kasantuwar kasashen musulmi da cigaban da yake acikin kasahsen musulmi da karkata ga addini da kihsin musulunci, da kin Amurka da kasashen turai, wani abu ne wanda za a yi alfahri da shi..

  Tare da la'akari da dukkan abin da muka yi bayani a sama, zamu iya tsinkayo  gushewar siyasa marar cin nasara ta kasashen yamma da samar da hadin kai tsakani al'ummar muslmi da samara da duniyar muslunci mai karfi.

  A halin yanzu Amurka da kasagshen Yamma da mabarnatan shugabannin haramtacciyar kasar Isra'il sun fahimci hakikanin farkawar al'ummar musulmi, sannan sun tabbatar da rashin amfanin karfin soja wajen fuskantar al'ummar muslmin, don haka ne suke bin hanyoyi daban-daban na siya da  dubaru don cimma mummunan gurinsu.

  Daya daga cikin hanyoyin da suke bi na dubaru a yau wajen cimma wannan guri nasu, shi ne haifar da sabani a cikin al'ummar musulmi, ta hanyoyi daban-daban wadanda suka hada da amfani da kudi da duk wata hanya wadda zata kai su ga gurinsu ta hanyar samar da sabani tsakanin musulmi ta yadda zasu dauke hankali musulmi ta hanyar sanya su rigima da junansu. Ta yadda zasu sake hada rigima da junanmu wadda zai iya kai ga kashe-kashe a tsakanin juna.

  A yau duk wani motsi na haifar da sabani a tsakanin musulmi wani  zunubi ne wanda yake komawa ga tarihi. Wadanda da gangan suke kafirta dinbin al'ummar musulmi, ta hanyar fakewa da wasu dalilai marasa tushe, wadanda suke aibanta akidun sauran al'ummar muslmi ta hanyar zato marar tusha, wadanda suke aibanta kwazon matasa musulmin Lebanon wadanda suke kasance abiin alfahri ga al'ummar musulmi, w3adanda suke aikin don faranta wa Amurka da gwamnatin sahayina, suna yin Magana akan wani hadari wanda suka kirkira da kansu wai shi mai suna (jaririrn watan shi'a) Abin da ake nufi da shi(wai wani hadari ne wanda zai faru ta hanyar samar da kashen Shi'a wadan suka hada Iran, Irak, Siriya, da Lebanon) wadanda suke  aiki don durkusar da kasar musulmin Irak, sannan su haifar da kashe juna da kawar da kwanciyar hankali a Irak, wadanda suke takura zababbiyar gwamnatin Palasdin,, ta kowace hanya. Ko sun sani ko ba su sani ba suna matsayin masu tafka mummunan laifi, sannan tarihin musulunci da al'ummar musulmi na nan gaba zasu yi Allah-wadai da wannan aiki nasu, sanann zai dauke su a masatyin 'yankoren makiya.

    Al'ummar musulmi na duniya baki daya su sani cewa, lokacin tozarta musulunci da mayar da musulmi koma baya ya riga ya wuce, sannan an riga an shi ga sabon yanayi. Sannan wanna mummunan tunani wanda yake nuna cewa kasashen musulmi dole ne su cigaba da kasamcewa a karkashin mulkin mallakar kasashen yamma wanda ya hada da siyasa da al'adu, sannan abinda ya shafi tunani da aikin dai-daiku da na al'umma dole ne ya kasance suna koyi ne da kasashen yamma, wannan ya riga ya kau acikin zukatan al'ummar musulmi, kuma wannan ya faru ne ta hanyar zalunci da jiji da kan kasashen yammacin duniya, ta yadda musulmi suka farka suka fahimci makircinsu.

  Kasashen yamma mussamman bayan kasantuwar Amurka a matsayin shugaba, ta hanyar zalunci a bayyane ayyuka da mu'amalar da ta saba wa hankali, da girmankai da jiji da kai marar iyaka na kasashen yamma, ya sanya kashen musulmi sun dauki wadannan kashen a matsayin masu  yaki da addininsu. Aikinsu dangane da Palasdin da kuma yadda suke mu'amala da haramtacciyar kasar Isra'il, sannar da matakan da suke dauka dangane da makaman kare dangi wanda kasar isra'il ta mallaka, sannan da matakain da suke dauka dangane da shirin makamashin nukiliya wnada bai shafi makami ba a iran, sannan da goyon bayan da suka nuna wa Isra'il wajen kai wa Lebanon hari, ta hanyar taimakon Isra'il da makamai da hanyoyin siyasa, sannan da nuna rashin goyon bayansu akan Kare kan da al'ummar Lebanon suke yi wa kansu daga kasar Isra'il, Sannan da tatsar da  suke yi a koda yaushe akan kasashen larabawa da bayar da taimakonsu ga kasar Isra'il, da nuna goyon bayansu ga masu tozarta addinin musulmunci, kai harda tozarcin wasu manya daga cikin shugabannnin yamma wadanda suka hada da (pop) shugaban kiristocin katolika akan addinin musulunci, sannan da daukar wanda ya yi bincike akan abin da ya shafi holokos da akidun yahudawan sahayina, a matsayin mai laifi, sannan kai hari da kasha dimbin al'ummar musulmi a Irak da sunan dimokradiyya, da ruguza gydaje da rayuwar al'ummar iraki duk da suna dimokradiyya, sannan fito na fito da da gwamnatin da al'umma suka zaba ta Palasdin, Irak, Da sauran kasashen Amurka ta kudu, da duk gwamnatocin da 'yan koren Amurka da kasashen yamma ba su su ke mulki ba. Guguwar yaki da ta'addanci, ta bangare guda kuma suna tattaunawa da bayar da taimako da kungiyoyin ta'addanci a Irak da sauran wurare.

  Irin wadannan ayyuka da suka saba wa hankali sun zama hujja ga al'ummar musulmi, sannan sun taimaka wajen farkar da al'ummar musulmi. A yau ko suna so ko ba su wani motsi mai karfi ya riga ya kunno kai a duniyar muslmi, sannan wannan motsin ne a lokacin da ya dace zai dawo da izza da mutunci al'ummar musulmi.

  Wannan  lokaci  yana matsayin mai karfafa hakan, don haka masana da malamai suna da wani muhimmin nauyi da ya hau kansu. Saboda haka duk wani saku saku da nuna halin ko in kula  zai iya janyo babbar asara ga al'ummar musulmi. Malaman addini bai kamata ba su yi shiru dangane da raba kan al'ummar musumi, hakanan masana kada su yi wata-wata wajen fadakar da matasa akan halin da al'ummar musulmi suke acikin, da kaucewa wannan tarko na makiya musulunci. Yan siyasa da shugabanni ya kamata su rike al'ummar su a wannan fage na fadakarwa, sannan su dogara da al'ummarsu, gwantocin musulmi ya kamata su kara samura da hadin kai a tsakaninsu, ta yadda zasu yi amfani da wannan karfi da suke da shi na hakika wajen yakar mulkin mallaka na kashaen yamma.

  A yau kungiyoyin leken asirin na Amurka da Emgila a iraki, Lebanon, da wasu daga cikin kasashen  Arewacin Afrika suna iya kokarinsu ta yadda zasu ga cewa sun samar da sabanin akida acikin al'ummar musulmi. Taron hajji ya kamata ya zama wani riga kafi ko magani akan wannan mummunan cuta da take bibiyarmu, Ayar nan da take cewa :"Ku bi Allah ku bi manzonsa, kuma kada ku yi jayayya a tsakaninku, sakamakon haka mutumcinku zai kau, kuma ku yi hakuri lallai Allah yana tare da masu hakuri".ya kamata ko yaushe ta kasance a gabanmu.

  A yau bara'a ga mushrikai wani kira ne wanda a cikin zukatan al'ummar musulmi.sannan taron aikin hajji wani taro ne wanda zai iya tabbatar da wannan kira wannda yake kunshe acikin halittar bil Adama.

  Ya kamata ku yi amfani da wannan dama, ku yi addu'a ga dukkan musulmi da yin addu'a don bayyanar Imam mahdi a.s. wanda zai yantar da al'ummar muslmi daga wannan bakin zaunci da suke cikinsa, sannan ku yi iya kokarinku don ku wanke kawunanku  acikin wannan teku.

  Ina rokon Allah da ya sanya ku dace acikin rayuwa ya kuma amsa maku hajjinku.

 

  

Sayyid Ali Khamna'i

3-12-1427